MUTUM BAKWAI DASUKAYI GWAGWARMAYAN SAMUN YAN CIN IS A KAI A NAJERIYA










Mutum bakwai da suka yi rawar gani wajen samun 'yancin Najeriya
1 Oktoba 2019
Aika wannan shafi Facebook  Aika wannan shafi WhatsApp  Aika wannan shafi Messenger  Aika wannan shafi Twitter  Aika
BBC ta yi bincike daga wurare daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Najeriya 'yanci. Mun kuma samu mutum bakwai da suka yi fice wadanda za mu bayyana takaitaccen tarihinsu da rawar da suka taka:
1. Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto(Yuni 12, 1910 - Janairu 15, 1966)
Sir Ahmadu BelloHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
An haifi Sir Ahmadu Bello a garin Rabbah na jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya. Sardauna na daya daga cikin jagororin Najeriya da suka yi fice a duniya. Ahmadu Bello ya rike sarautar Sardaunan Sokoto kuma ya jagoranci jam'iyyar Northern People's Congress, NPC, inda ya mamaye harkar siyasar kasar a jamhuriya ta daya. Sir Ahmadu Bello ya yi fafutuka wajen nema wa Najeriya 'yanci, inda bayan dawowarsa daga wani bulaguro da ya yi zuwa Birtaniya, aka nada shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar lardin Sokoto. A yau hoton Sardauna ne a kan kudin Najeriya na ₦200.
TALLA

Wasu daga cikin abubuwan da ake tunawa da Sardauna sun hada da Jami'ar Ahmadu Bello University da ke Zaria wadda aka sanya mata sunansa da kuma rawar da ya taka wajen ci gaban arewacin kasar.
2. Chief Anthony Enahoro (22 Yuli 1923 - 15 Disamba 2010)
Chief Anthony EnahoroHakkin mallakar hotoGOOGLE
Cif Anthony Eromosele Enahoro na daya daga cikin fitattun 'yan gwawarmayar kin jinin mulkin mallaka kuma mai rajin kafa dimokradiyya. Mista Enahoro ya zama Editan jaridar Southern Nigerian Defender ta Nnamdi Azikiwe, inda ya zamo editan jarida mafi karancin shekaru a Najeriya. Enahoro ne mutum na farko da ya fara mika bukatar neman 'yancin kan Najeriya a 953. Hakan ne ya sa ake yi masa lakabi da "Uban Najeriya". Chief Enahoro masani ne kuma ya yi ta fafutuka kan Najeriya har lokacin da ya mutu a 2010.
3. Herbert Macaulay (14 Nuwamba 1864 - 7 Mayu 1946)
Herbert MacaulayHakkin mallakar hotoGOOGLE
Sunansa Olayinka Herbert Samuel Heelas Badmus. Ya kasance dan kishin kasa, dan siyasa, Injiniya, mai ilimin tsara gine-gine kuma dan jarida ne kuma mawaki. 'Yan Najeriya da dama na bayyana shi da jagoran masu kishin kasar.
Mista Macaulay ya yi suna wajen hamayya da mulkin turawan mulkin mallaka. A shekarar 1919, ya tsaya wa masu sarauta a London wadanda aka kwace wa gonaki inda ya tilasta wa gwamnatin turawan mallaka da ta biya sarakan diyya.
Hakan ne ya fusata Majalisar Birtaniya ta British Council inda har ta kai ga ta daure shi sau biyu. Macaulay ya shahara inda a ranar 24 ga watan Yuni 1923 ya kafa jam'iyyar siyasa ta farko a Najerita ta Nigerian National Democratic Party (NNDP). Herbert Macaulay ya mutu a 1946 to amma hotonsa ne a tsohuwar ₦1.
4. Chif Obafemi Awolowo (6 Maris 1909 - 9 Mayu 1987)
Chief Obafemi AwolowoHakkin mallakar hotoBETTMANN
Chif Obafemi Jeremiah Oyeniyi Awolowo dan kishin kasa ne kuma dattijo wanda ya taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar neman 'yancin kan Najeriya. Shi ne firimiyan yankin kudu maso yammacin Najeriya na farko sannan ya yi kwamishinan kudi a gwamnatin tarayya. Chif Obafemi ya zama mataimakin shugaban kasa na majalisar zartarwa a lokacin yakin basasa. Awolowo ya jagoranci masu hamayya na jam'iyyar Action Group a majalisar dokokin tarayya. Duk da cewa bai ci takarar shugabancin Najeriya a jamhuriya ta biyu ba, Cif Awolowo ya kasance dan takara na biyu mai yawan kuri'a bayan Alhaji Shehu Shagari. Hoton Obafemi ne a jikin ₦100.
5. Funmilayo Ransom Kuti (25 Oktoba 1900 - 13 Afrilu 1978)
FumilayoHakkin mallakar hotoGOOGLE
Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace daya tilo a jerin sunayen 'yan gwagwarmayar neman 'yancin kan Najeriya. Fumilayo ta kasance malamar makaranta, 'yar siyasa, mai fafutukar kare 'yancin mata sannan kuma mai rike da sarautar gargajiya. Ita ce mahaifiya ga shahararren mawakin nan na Najeriya, Femi Kuti. Funmilayo ce mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya. An zabe ta a majalisar sarakunan gargajiya, inda ta kasance wata wakiliya ta al'ummar Yarabawa. Fafutukar da ta yi ta janyo wa 'ya'yanta bakin jini musamman lokacin gwamnatocin soji.
6. Nnamdi Azikwe (16 Nuwamba 1904 - 11 Mayu 1996)
Sir Ahmadu Bello da Chief Obafemi Owolowo da Dr Nnamdi AzikweHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Chif Benjamin Nnamdi Azikiwe ne jagoran 'yan gwagwarmayar masu kishin kasa na zamani. Nnamdi wanda ake yi wa lakabi da mai kishin kasa ya rike Editan jaridar African Morning Post. Shi ne mutum farko dan Najeriya da sunansa ya shiga Majalisar Tuntuba ta Amurka. Bayan ayyana Najeriya a matsayin Jamhuriya, Dr Nnamdi Azikwe ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya hada kan kasar. Dr Zik ya zamo shugaban Najeriya na farko.
7. Tafawa Balewa (Disamba 1912 - 15 Janairu 1966)
Tafawa BalewaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa ne firai ministan Najeriya na farko nayam da kasar ta samu 'yancin kai a 1960. An zabi Sir Abubakar Balewa a matsayin dan majalisar dokokin lardin arewa a 1946, sannan ya je majalisar dokoki ta tarayya a 1947. Tafawa Balewa ya zamo dan majalisa mai rajin kare arewacin Najeriya. Alhaji Abubakar Tafawa Balewa tare da Sardaunan Sakkwato sun kafa jam'iyyar Northern People's Congress (

Comments

Popular posts from this blog

WASU FITATTUN KABILAR KANURI DASUKA SHAHARA A DUNIYA

TAKAITACCEN TARIHIN KASAR HAUSA the DA KASASHEN DASUKA YADU HAR IZUWA YAU

YADDA ZAKA SAMU KUDI SAMADA DA 20K AKAN 1,400 KACHAL👌 A WAYAR KA TA ADROIN K