TAKAITACCEN TARIHIN KASAR HAUSA the DA KASASHEN DASUKA YADU HAR IZUWA YAU
Al'ummar Hausa dai, al'umma ce dake zaune a arewa maso
yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin
jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai dimbin yawa, sun bazu a
cikin kasashen Afirka da kasashen Larabawa kuma a
al'adance masu matukar hazaka, akalla akwai sama da
mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shi ne
asalin yarensu. A tarihi kabilar Hausawa na tattare a
salasalar birane. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne
tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da
dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma
Fulani .
A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa
ke yunkurin kawar da mulkin Aringizo na Fulani , sai
Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya suka mamaye
arewancin Nijeriya , da kuma kafa manufofin mulkin bayan
gida, a bisa karkashen mulkin Birtaniya ,'yan mulkin mallaka
sai suka marawa Fulani baya na cigaba da manufofin
Aringizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza
tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a
arewacin Nijeriya .
Kodayake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da
zuwan Addinin Musulunci da kuma karbarsa da hannu
bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.
Ginshikokin al'adun Hausawa na da mutukar jarunta,
kwarewa da sanayya fiye da sauran al'ummar dake
kewayenta.
Daura Kasace wacce a kasani mai dadewa da tarihi a kasar
Hausawa.
Sana'ar noma ita ce babbar sana'ar Hausawa, sabo da
ingancin noma; Hausawa ke wa sana'ar noma kirari da
cewa, "na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya
tarar" , akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima
watau harkar fatu, rini, sa'a da kira, fannonin dake
mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in Hausawa.
Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci
kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da
kullum, tare da masu mulki da masana.
Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanayyar
harshe a nahiyar Afirka , harshen hausa ya aro wasu
kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci kana kuma
harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa
al'adar cudeni-in cudeka. Harshen Hausa dai ya zama
harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa
bane a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a
manyan biranen yammacin Afirka da arewacin Afirka da
kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma
yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa
aikin Hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da
kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka
buga tun kafin zuwan Turawa 'yan mulkin mallaka na
Birtaniya . Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da
aka kirkiro tun kafin zuwan Turawa, da ba kasafai ake
amfani da shi ba yanzu.
Kasashen da Hausawa suka
yadu
kasashen Larabawa sune wadannan :-
kasar Burkina faso
kasar Kameru
kasar Aljeriya
kasar Benin
kasar Cadi
kasar Gambiya
kasar Ghana
kasar Togo
kasar Gine-Bisau
kasar Mali
kasar Sierra Leone
kasar Gabon
kasar afirka ta tsakiya
kasar Libya
kasar Ethiopia
kasar Kwango (JDK)
kasar sudan
kasar Saudiyya
Ire-Iren 'Yaren Hausa
'Yaren Hausa yana da ire-ire da yawa gabashin Hausa su
ne :-
Gabashin Hausa
Kanawa
Kataguwa
Hadejawa
Gumelawa
(( katsinawa))
Yammacin Hausa
Daurawa
Sakkwatawa
Katsinawa
Kurfayawa
Gobirawa
Adarawa
Kebbawa
Zamfarawa
Arewacin Hausa
Arewa
Arawa
Hausa ajami wanda suka fita daga kasashen Hausa suka
shiga kasashen Larabawa shekaru aru-aru harma sun isa
kasashen Turai kuma sunada sarkin Hausawan Turai nafarko
wato Sarki Sirajo Jan Kado:-
Sarkin Hausawan Turai nafarko Sirajo Jan
Kado
Sudan
Saudiya
Libya
Comments
Post a Comment