TAKAITACCEN TARIHIN HAUSA BAKWAI DA BANZA BAKWAI
Tarihin Hausa bakwai da banza bakwai A ƙarni na 13 ne dai ƙasar Hausa tayi tashe harma take gasa da Daular Kanem-Borno da Mali. Haka kuma ƙasar Hausa ta yi fice wajen cinikin Zinari da Goro da Gishiri da fatu da ƙiraƙi da kuma leda. Daga shekarar 1804 zuwa 1808 kuma Shehu Usmanu Ɗan fodio ta yarda suka kasance a ƙarƙashin Dular Shehu Usmanu Ɗan fodio. Garuruwan Hausa bakwai da Banza bakwai sun samo asali ne daga Auren Sarauniya Daurama ta Daura da kuma Umarun Baghadaza wanda aka fi sani da Bayajidda wanda tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya nuna cewar wani Jarumi ne daya fito daga ƙasar Baghadaza. Da farko dai an ce Bayajidda ya fara yada zango ne a ƙasar Borno inda yake taimakawa Shehun wajen yaƙi kuma har takai ya auri ɗiyar shehun Borno na wancan lokaci. Koda yake ya bar Borno bayan da aka zargeshi da nema ƙwace sarautar Borno kafin daga bisani ya taho ƙasar Daura. Koda yake kuma kafin ya zo Dauran ya fara yada zango a Garun Gabas da ke ƙasar Hadeja inda aka ce ita wannan ma