MUTUM BAKWAI DASUKAYI GWAGWARMAYAN SAMUN YAN CIN IS A KAI A NAJERIYA
Mutum bakwai da suka yi rawar gani wajen samun 'yancin Najeriya 1 Oktoba 2019 Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi WhatsApp Aika wannan shafi Messenger Aika wannan shafi Twitter Aika BBC ta yi bincike daga wurare daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Najeriya 'yanci. Mun kuma samu mutum bakwai da suka yi fice wadanda za mu bayyana takaitaccen tarihinsu da rawar da suka taka: 1. Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto(Yuni 12, 1910 - Janairu 15, 1966) Sir Ahmadu BelloHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES An haifi Sir Ahmadu Bello a garin Rabbah na jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya. Sardauna na daya daga cikin jagororin Najeriya da suka yi fice a duniya. Ahmadu Bello ya rike sarautar Sardaunan Sokoto kuma ya jagoranci jam'iyyar Northern People's Congress, NPC, inda ya mamaye harkar siyasar kasar a jamhuriya ta daya. Sir Ahmadu Bello ya yi fafutuka wajen nema wa Najeriya 'yanci, inda bayan dawowarsa d